24/08/2025
TAKAITACCEN TARIHIN SHAHID MUHAMMMAD KABIR (Shahidi na Uku A harka islamiyya).
Anhaifi shaheed muhammad kabir a shekarar 1979 a garin Garko cikin garin Rimi dake Jihar Kano. Ya tashi hannun mahaifansa malama Ami da mahaifinsa malam Kabir.. Muhammad yayi karatun primary, inda yana matakin Secondary a dan rimi ya samu Shahada.
Idan ana maganar matasa ko yara masu karancin shekaru da s**a yi shahada a Harkar Musulunci ta kasar nan to sunan Shahid Muhammad Kabir shi zai zo a na farko, domin kuwa ya sami shahada ne a lokacin da yake dan shekaru 14 da haihuwa.
Yadda lamarin ya faru kuwa shi ne a ranar Juma'a 9 ga Afrilu 1993 Shahid Muhammad tare da 'yan uwansa dalibai na sakandaren Rimi ta jihar Kano sun halarci wani wa'azi da dan uwa kuma Malami, Malam Ibrahim ya gabatar a masallacin. Can sai 'yan sanda s**a bayyana s**a rika harba tiya gas, s**a k**a wanda ya yi wa'azin. Daga nan ne fa daliban s**a rika yin takbir suna cewa "Ba mu yarda ba."
Kwatsam sai ga 'yan banga dauke da muggan mak**ai irinsu adda, takobi, gariyo, kokara da sauransu sun dira s**a shiga bugun wadannan dalibai.
Nan take s**a raunata 'yan uwa musulmi da dama. Shahid Muhammad kuwa s**a karya masa kwankwaso. Baya ga nan sun yi masa mummunan sara da ta sa da kyar aka iya gane ko waye shi.
Bincike ya tabbatar da cewa shugaban Karamar Hukumar Rimi na lokacin, Aliyu Yahya Rimi da Kansilan ayyuka na Karamar Hukumar, Sabo Aliyu Rimi suna da hannu dumu-dumu a wannan kisa. Haka ma wani wai shi Alhaji Isuhu. Su s**a ba 'yan bangar izinin yin ta'addancinsu.
Malam Zakzaky ya tura wata tawaga don yin ta'aziyya ga iyayen yaron da ke garinsu Garko a cikin jihar Kano. Baffan Shahid din kuma Na'ibin Limamin garin, shi ya yi magana a madadin 'yan uwan Shahid din. Inda ya nuna godiyarsa ga Malam Zakzaky da sauran 'yan uwa musulmi saboda yadda s**a nuna damuwarsu ga abin da ya faru.
Ita kuwa mahaifiyar Kabir ta bayyana danta da cewa "Yaro ne mai biyayya gare ni. Duk aikin da na sa shi sai ya yi, kuma duk i