19/04/2026
Rawar da zamu iya takawa domin rage hauhawar mace-macen Aure a Arewa:
Rubutu: Auwalu Hussaini daga Birnin Damaturu
Lahadi: 19-04-2026
La'akari da yadda Aurarraki ke yawan mutuwa babu kakkautawa, ba dare ba rana, yake yaduwa k**ar wutar daji, akwai bukatar kowanne daga cikinmu ya tashi tsaye ya bayar da kowacce irin gudunmowa wajen rage wannan annoba da tataso al'ummarmu agaba.
Akwai Auren da yake mutuwa kasa da wata daya kacal da daura shi. Wani watanni uku, wani watanni shida. Masu kaiwa shekara ko su haura shekaru basu da yawa.
Wasu aurarrakin kuma, koda ba'akai ga matakin saki ba, zaka ga yawan je-dawo, gutsiri-tsoma da kace-nace tsakanin Ma'auratan da Iyayensu ko masu ruwa-da-tsaki acikin auren kowa hankalinsa a tashe.
Wasu matan ayanzu da nake wannan bayani, sunacan jibge a gidajen iyayensu; auren baiyi rai ba, shi bai mutu ba.
Wasu matan da auren akansu amma yanzu haka da nake wannan jawabi sun shiga bariki suna gidajen magajiya, wasu ba'a ma san inda suke ba. Su ba sakakku ba, su ba masu aure ba.
Wasu Ma'auratan yanzu haka suna kwance a gadajen asibitoci saboda larurar hawan-jini ko ciwon zuciya. Wasu kuma saboda raunuka da mak**ai da s**a samu daga gidajen auren.
Wasu, yanzu haka suna daure a gidajen yari suna jiran hukunci saboda kashe matansu ko mazansu na aure.
Wasu suna zaune tare, auren bai mutu ba amma kowa jini ya kume masa a karkashin zuciya saboda takaici da bakincikin da yake kunsa daga abokin zamansa wanda yak**ata ace shine yafi kowa samar masa kwanciyar hankali da cikakkiyar natsuwa k**ar yadda Allah Madaukakin Sarki ya fada cikin Suratur Rum, Aya ta 21:
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا لِّتَسۡكُنُوٓاْ إِلَيۡهَا وَجَعَلَ بَيۡنَكُم مَّوَدَّةٗ وَرَحۡمَةًۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Bi ma'ana: Na daga cikin Ayoyin Allah Madaukaki halittar Mace daga jikin Namiji domin samarwa juna soyayya da tausayi dake kawo natsuwa...idan aka yi filla-filla da Ayar.
A matsayina na almajiri bari natsaya anan. Sauran bayani muje wajen Malamai.
A haka, da dama sun kwanta barci sai gawawwakinsu aka dauka da safe. Bakincikin zaman tare ya karasa su cikin ruwan sanyi.
SHIN WAI INA MATSALAR TAKE?
Duk muna da laifi da gagarumar gudunmowa da muke badawa a tabarbarewar wannan al'amari. Saidai idan mutum bai fidda son zuciya ba, ba lallai ne ya yarda yana bayarda gudunmowar kai-tsaye ko a fakaice ba.
Kowa yasan me nake nufi anan. Saboda haka, ba bayani zanyi akan dalilai ko sabubban dake lalata aurarraki ba, a'a. Zan lissafo wasu matakai ne da a tawa karamar fahimtar cikin-cokali idan aka dube su, aka dauki matakai akansu, k**ar za'a iya samun saukin wannan babbar annobar dake haddasa mana masifu da bala'o'i iri-iri da ba zasu kirgu ba. K**a daga lalacewar yara, gurbacewar tarbiyya, yawaitar zinace-zinace, shayeshaye da kisan-mummuke wanda hakan ke taka muhimmiyar rawa wajen rugurguza mana tattalin arziki da rashin albarkar zamantakewa.
💥 Mu taimakawa juna mu yada wannan sako domin ya isa inda muke bukata.
Shiga sashen muhawara (Comments Section) domin ganin wa'yannan matakai guda biyar (5) rak da idan mukayi tsayin daka akansu, zamu iya samun sauki sosai, idan muka tsarkake zukata da taimakon Allah Madaukakin Sarki 👇
GreatestHighlights