25/07/2024
TSAYUWA DA TASHI A KARATUN AL-ƘUR'ANI
A tilawar Al-ƙur’ani akwai abun da ake kira “الوقف والابتداء”; wato ilmin da ta hanyar sa ake sanin wurin da ya k**ata a tsaya da wurin da bai k**ata ba, wurin da ya k**ata a k**a karatu da wurin da bai k**ata ba.
Wannan fanni ne a Tajwidi mai faɗin gaske, domin kafin mutum ya ƙware a kan sa yana buƙatar abubuwa guda biyu:
1. Ilmin Larabci [Nahawu]
2. Ilmin Tafsirin Alqur'ani [daidai gwargwado]
Rashin ilmin “alwaƙfu wal-ibtidaa'” yana da illa sosai domin mutum yakan canza ma'anar aya, ko ma ya canza hukunci daga misali, halal zuwa haram.
Don muhimmancin wannan ilmin Mallaman Tajwidi da dama sun keɓance shi da wallafa ta yadda aka wallafa littatafai da yawa a kai.
Ash-Shaikhul Husariy ya rubuta littafi sukutum a kan wannan ilmin wanda ya saka masa suna “معالم الاهتداء إلى معرفة الوقف والابتداء”. Ya yi bayani sosai a ciki.
Al-Imamu Ibnul Jazariy yana cewa a cikin “Almuƙaddimatul Jazariyyah” a ƙarƙashin “باب معرفة الوقف والابتداء”.
“وبعد تجويدك للحروف — لا بد من معرفة الوقوف”
Ma'ana: bayan ka koyi taɗbiƙin harufa, ka iya karatu da Tajwidi daidai gwargwado, toh abun da yake kan ka na gaba shi ne ka nemi ilmin “alwaqfu wal-ibtidaa'”, babu makawa daga wannan.
Saboda haka, ƴan’uwa na ɗaliban Alqur'ani sai mu himmatu da wannan, saboda kyawun karatu ba iya fitar da harufa da kyau ba ne. Kalmar “Tajwidi” ta game komai; iya taɗbiƙi, sanin wurin tsayuwa, sanin wurin tashi, sanin ladubban karatu, dss.
Idan kana karatu ba duk inda ka ga dama ake tsayawa ba, ba kuma sai inda numfashin ka ya tsaya ba. Sannan ka dinga bin tsayuwar mus'hafi, Mallamai sun riga sun yi mana mafi rinjayen aikin.